‘Yan Sanda a jihar Borno a ranar Talata sun tabbatar da mutuwar ‘yan kungiyar gora da aka fi sani da C-JTF su uku tare da jikkata mutane 17 a dalilin wani harin kunar bakin wake da wani mutum yakai akan keke a birnin Maiduguri.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Borno, Joseph Kwaji, ya bayyana a wata sanarwa da ya fitar a Maiduguri,inda ya bayyana cewar lamarin ya auku ne da misalin karfe 8:30 na dare a Muna Delti, wani waje dake bayan cikin birnin Maiduguri.

Mista Kwaji ya bayyana cewar, dan kunar bakin waken yana tafiya ne akan keke a lokacin da ya tayar da Bom din dake jikinsa, inda ya kashe kansa nan take, tare da wasu mutum uku ‘yan kungiyar gora ta jihar Borno.

Ya kara da cewar, akalla mutane 17 sun samu raunuka a sanadiyar wannan hari. ya cigaba da cewar, wadan da suka samu raunuka an samu kwashe su zuwa asibitin koyarwa na jami’ar Maiduguri domin basu kulawa ta gaggawa.

A cewarsa, masu kwance bamabamai na musamman na rundunar ‘yan sanda tuni suka mamaye yankin da abin ya auku domin bayar da kariya da kuma tabbatar  da cewar mutane sun vigaba da walwala kamar yadda suka saba.

NAN

LEAVE A REPLY