Shugaba Muhammadu Buhari
Daga Hassan Y.A. Malik

 

Wani Qudus Ahmed wanda sakatare ne a kungiyar yakin neman zaben Buhari (BCO) ya samu muggan raunika da suka hada da yanka a kan shi da wasu sassan jikin shi a yayin zaben shugabannin jam’iyyar APC da aka yi a jahar Kwara a jiya Asabar.

Rahotanni sun bayyana yadda aka yi wa wasu daga cikin mambobin jam’iyyar dukan tsiya a lokacin zaben wanda aka yi a Illorin, babban birnin jahar.

Rikicin ya fara ne a yayin da wani bangare na jam’iyyar wanda ya riga ya biya kudin neman zaben a banki ya bukaci a bashi takardar neman zabe a sakateriyar jam’iyyar ta jahar, lamarin da ya ci tura.

Bangare daya na jam’iyyar ya fadawa mambobin daya bagaren cewa takardun ba sa cikin ofishin, inda daga nan ne aka fara hayaniya.

Yayin da ‘yan jam’iyyar ke barin sakateriyar ne wasu ‘yan banga suka afka masu da sara da suka, lamarin da ya haifar da jikkatar da dama daga cikin su a ciki har da Qudus.

LEAVE A REPLY