Atiku Abubakar

Tsohon mataimakin Shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar, yayi Allah wadai da hare haren da aka kai a Adamawa ranar talata, harin da yayi sanadiyar mutuwar mutane 14, ciki kuwa har da wani kakakin jam’iyyar PDP na jihar Adamawa, Sam Zadok.

Atiku a wata sanarwa da ofishinsa ya fitar a Abuja a ranar laraba, ya kuma yi Allah wadai da irin abinda ya faru a jihar Kaduna, dama duk sauran inda ake kai hare hare na babu gaira babu dalili, wanda hakan ke janyo asarar rayuka babu gaira babu dalili.

Ya nuna matukar kaduwarka da irin wadannan abubuwan da suke faruwa, irin yadda ake rasa rayuka babu ji babu gani akasar nan.  Hare haren daukar fansa dakuma batun kabilanci da suke sabbaba hasarar rayuka abu ne da ba zamu lamunta ba.

Akwai laifin Shugabanni kwarai da gaske akan irin yadda suka bari irin wadannan abubuwa da suke neman rincabewa su zamewa kasarnan wani irin abu mai wuyar sha’ani.

“Bukatarmu ta dunkulewa waje daya tafi muhimmanci sama da kasancewarmua rarrabe”

Bayan haka kuma, Atiku Abubakar ya jajantawa jam’iyyar PDP bisa wannan rashi da suka yi na kakakin jam’iyyar.

LEAVE A REPLY