Tsohon mataimakin Shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar

Tsohon mataimakin Shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana komawarsa tsohuwar jam’iyyarsa ta PDP a ranar lahadi a wani sakon bidiyo da ya fitar. Atikun ya koma PDP ne bayan da ya sallama jam’iyyar APC a makon da ya gabata, Atikun ya bayyana komawarsa PDP da cewar da sabon gini gara yaɓe.

Atikun ya bayyana dalilin ficewarsa daga cikin jam’iyyar APC da cewar, ba a kama hanyar cika alkawuran da aka daukarwa ‘yan Najeriya a yayin kamfen din zaben 2015 ba. Atiku Abubakar ya bayyana rashin gamsuwarsa kan yadda dubban matasa suke zaune kara zube babu aikin yi, yayin da APC ta nuna ko in kula kna hakan.

“Babban burina shi ne, naga an samarwa matasa aikin yi a Najeriya, muna da tarin matasan da suka kammala karatu suna nan zaune basu da aikin fari balle na baki” A cewar Atiku Abubakar.

Shin ya kuke kallon wannan komawar da Atiku ABubakar yayi zuwa jam’iyyar PDP?

LEAVE A REPLY