Sabon zababben Shugaban jam'iyyar PDP na kasa, Uche Secondus

Uche Secondus ne ya lashe zaɓen Shugaban jam’iyyar PDP na ƙasa da aka gudanar a daren jiya Asabar a filin eagle sukwaya dake birnin tarayya Abuja. Wannan dai shi ne babban taron jam’iyyar PDP na ƙasa wanda a cikinsa aka zabi sabbin Shugabannin jam’iyyar wadan da zasu ja ragamarta hae zuwa shekaru hudu nan gaba.

Uche Secondus wanda ya taba rike muƙamin Shugabancin riƙo na jam’iyyar bayan kammala zaben 2015, wanda jam’iyyar ta sha kaye. Uche ya lashe zaben ne da gagarumin rinjaye inda ya doke abokan karawarsa Tunde Adeniran da kuma Reymond Dokpesi da gagarumar rata. Ya samu a kalla kuri’u 2000 yayinda Tunde Adeniran yake binsa da 230 sai Reymond Dokpesi da kuri’a 66.

Sannan kuma an zabi sauran Shugabannin jam’iyyar da suka hada da mataimakin Shugaban jam’iyyar mai wakiltar shiyyar Arewa Sanata Babayo Garba Gamawa sai kuma mataimaki mai wakiltar kudancin Najeriya Yemi Akinwomi, sannan sai mukamin babban sakataren jam’iyyar wanda aka zabi Sanata Umaru Tsauri.

Sauran su ne, mataimakin sakatare Abubakar Mustapha, sai Babban ma’ajin kudi Aribsala Adewale da mataimakinsa Wada Masu, da kuma Sakataren kudi Abdullahi Maibasira da mataimakinsa Irona Gerald da kuma babban sakataren tsare tsare Austin Akobundu da mataimakinsa Hassan Yakubu.

Sauran sunhada da, Kakakin jam’iyyar na kasa Kola Alogbondiyan da mataimakinsa Dira Odeyemi da mai baiwa jam’iyyar shawara ta fuskar Shar’ah Ahmed Liman da mai binciken kudi Adamu Mustapha da mataimakinsa Divine Arong da Shugabar mata Mariya Waziri da mataimakiyarta Hadizat Umoru. Ragowar su ne, Shugaban matasa Udeh Okoye da mataimakinsa Umar Maina.

Tuni dai sabbin Shugabannin da aka zaba suka sha rantsuwar kama aiki, bayan da aka bayyana su a matsayin zababbun Shugabannin jam’iyyar na kasa. A jawabinsa yayin da ya gama shan rantsuwa, sabon Shugaban jam’iyyar Uche Secondus, yayi godiya ga wadan da suka zabe shi, sannan yayi kira da a bashi goyon baya domin kai jam’iyyar ga nasara a babban zaben da take tunkara na kasa a 2019.

LEAVE A REPLY