Gwamnan jihar Legas Akinwunmi Ambode ya kaddamar da mutumin mutumin marigayi Cif MKO Abiola a unguwar Alapere, Ketu dake jihar Legas. Gwamnan ya kaddamar da wannan mutum mutumi ne a cigaba da bukukuwan tunawa da ranar da aka yi zaben 12 Yunin 1993.

Tuni dai Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ayyana baiwa marigayi Cif MKO Abiola lambar girma ta kasa mafi girma da daraja wato GCFR, yayin da dantakarar mataimakinsa Babagna Kingibe ya rabauta da lambar GCON.

Haka kuma, tuni Shugaban kasa ya ayyana ranar 12 ga watan Yuni a matsayin sabuwar ranar tunawa da demokaradiyya a Najeriya.

Jagoran jam’iyyar APC na kasa, Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewar baiwa Abiola lambar girma ta kasa mafi girma ya nuna cewar karara shi ne ya lashe zaben 12 Yuni da aka yi a shekarar 1993.

LEAVE A REPLY