Gwamnan jihar Zamfara, kuma shugaban kungiyar Gwamnonin Najeriya, Abdulaziz Yari Abubakar yayin da yakke Marabtar tsohon SHugaban jam'iyyar PDP na kasa da ya sauya sheka zuwa jam'iyyar APC a fadar SHugaban kasa domin yin wata ganawa ta musamman tare da SHugaba Muhammadu Buhari

Tsohon Shugaban jam’iyyar PDP na kasa Sanata Ali Modu Sheriff, wanda ya fice daga jam’iyyar PDP ya koma jam’iyyar APC a makonnin da suka wuce, yana yin wata ganawa ta musamman da Shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar Shugaban kasa dake Aso Villa a Abuja.

Tsohon Gwamnan jihar Borno kuma tsohon Shugaban jam’iyyar PDP, ya shiga takun saka da tsohuwar jam’iyyar tasa ne lokacin da ya kai jam’iyyar kara kotu kan batun Shugabancin jam’iyyar.

Daga bisani dai kotu ta yi hukunci kan Shugabancin jam’iyyar inda tace Ali Modu Sheriff ba cancanci cigaba da rikon Shugabancin jam’iyyar ba.

A halin yanzu yana yin wata ganawa ta sirri tare da Shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar Shugaban kasa.

LEAVE A REPLY