Tsohon Gwamnan jihar Kebbi da ya sauya sheka zuwa jam'iyyar APC daga PDP.

Tsohon Gwamnana jihar Kebbi, Saidu Usman Nasamu Dakingari, a ranar Asabar tare da magoya bayansa sama da dari biyu suka sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa jam’iyya mai mulki ta APC.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya, NAN, ya ruwaito cewar tsohon Gwamnan na jihar Kebbi tare da mataimakinsa wanda suka yi mulki karo biyu a karkashin inuwar jam’iyyar PDP, sun bayyana goyon bayansu ga jam’iyyar APC mai mulkin jihar.

Shugaban jam’iyyar APC na jihar Kebbi, Attahiru Maccido, shi ne ya karbe su tare da dafawar Gwamnan jihar Atiku Abubakar Baguda a wani kasaitaccen biki da aka yi a Birnin Kebbi.

“A cewarsu, sun koma jam’iyyar ta APC ne, sabida irin yana yin Shugabancin adalci na Shugaban kasa Muhammadu Buhari da kuma Gwamnan jihar Atiku Bagudu, musamman ta fannin tsaro da bunkasa aikin noma da kuma habakar tattalin arki”

Shugaban jam’iyyar ya tabbatarwa da tsohon Gwamnan da tawagarsa da suka sauya sheka cewar, wannan komawar ta su zuwa jam’iyyar APC ta nuna irin shugabancin gaskiya da Gwamnan jihar yayi na tsawon shekaru uku a jihar.

A lokacin da yake magana a madadin wadan da suka sauya shekar, tsohon Gwamnan Kebbi Saidu Dakingari, yace wannan sauya sheka ta biyo bayan dogon nazarin da yayi tun bayan da ya bar mulki.

“Tun da na bar mulki tsawon Shekara uku, babu wanda ya taba jin muryata kan wani batu da ya shafi siyasar jihar Kebbi, na koma jam’iyyar APC ba dan ayi mun wani abu ba,illa gamsuwa da salon Shugabanci na Shugaban kasa Muhammadu Buhari da kuma Gwamnan jihar Kebbi Atiku Bagudu wanda suke gudanar da Shugabanci abin koyi”

“A sabida haka nake neman gafarar dukkan wadan da na batawa ko nayi musu ba daidai ba, ina kuma tabbatarwa da kowa cewar na yafewa dukkan wanda ya bata min”

Alokacin da yake nasa jawabin, Gwamnan jihar Kebbi Atiku Abubakar Bagudu, ya bayyana jin dadinsa inda yace, a yanzu jihar zata taifi bai daya cikin nasara tare da zuwan wadannan gaggan mutane da suka shigo jam’iyyar.

“Jiharmu ta Kebbi, Allah ya albarkace ta da albarkatun kasa, amma yadda zamu fi safarar su zuwa kasashen waje domin alfanun jihar ya zamar mana alakakai”

“Tare da hadin kan wadan da suka shigo wannan jam’iyya tamu, zamu samu bunkasa da cigaba cikin sauri idan har da gaske muna kishin jiharmu”

Mataimakin Shugaban jam’iyyar APC da yake kula da yankin Arewa Maso Yamma, Inuwa Abdulkadir, ya yabawa wadan da suka sauya shekar, inda yayi musu fatan alheri.

Ya bayyana cewar, irin ayyukan cigaba da Gwamna Bagudu yayi a jihar su ne suka sanya mutane suke tururuwar shigowa jam’iyyar APC a jihar.

NAN ta ruwaito cewar, jiga jigan jam’iyyar adawa ta PDP da suka sauya sheka zuwa APC sun hada da Sakataren Gwamnatin jihar karkashin Saidu Dakingari, Rabiu Kamba, da tsohon dan majalisar wakilai ta tarayya Sani Kalgo da Abdullahi Dan-Alkali da Haruna Hassan da kuma Halima Tukur.

NAN

LEAVE A REPLY