Tsohon Gwamnan jihar Kaduna Alhaji Lawal Kaita

Allah ya yiwa tsohon Gwamnan jihar Kaduna Alhaji Lawal Kaita rasuwa yana mai shekaru 85 bayan ya sha fama da jinya.

Iyalan tsohon Gwamnan sun bayar da sanarwar rasuwar tasa, inda suka ce, ya rasu a asibitin Turkawa dake Abuja mai suna Nizamieye, bayan ya shafe makwanni a sashin bayar da agajin gaggawa na asibitin.

An haifi Lawal Kaita a shekarar 1932 a Katsina. An zabe shi Gwamnan jihar Kaduna a karkashin tsohuwar rusasshiyar jam’iyyar NPN, yayi Gwamna daga Oktoba zuwa Disambar 1983 a lokacin da Soja suka yi juyin Mulki.

An zabi Lawal Kaita a matsayin mamba a majalisar rubuta kundin tsarin mulki ta kasa a shekarar (1977-1979), inda daga bisani ya zama mai baiwa tsohon Shugaban kasa Shehu Shagiri shawara na musamman.

Ya kuma tsayawa takarar Gwamnan jihar Kaduna karkashin inuwar jam’iyyar PRP, wadda Alhaji Abdulkadir Balarabe Musa ya kayar da shi a zaben fidda gwania shekarar 1979, zamanin jamhuriyar ta biyu.

Alhaji Lawal Kaita, na daga cikin ‘yn gaba gaba a ‘yan siyasar marigayi Shehu Musa YarAdua, haka kuma, yana daga cikin mutanan da aka kafa tsohuwar rusasshiyar jam’iyyar ACN da shi.

LEAVE A REPLY