Tsaffin sabuwar ‘yan PDP sun janye ganawa da mataimakin Shugaban kasa yemi Osinbajo. A ranar Litinin din nan ne aka shirya ganawa tsakanin tsaffin ‘yan sabuwar PDP din da matamaikin Shugaban kasa domin dinke barakar dake tsakaninsu da bangaren Gwamnati.

Sai dai baya ta haihu, domin kuwa a wata sabuwar sanarwa da Shugaban tsagin tsaffin ‘yan sabuwar PDP din Alhaji Kawu Baraje ya rabawa manema labarai ya bayyana cewar sun janye daga ganawa da mataimakin Shugabankasar kan abinda ya kira bita da kulli da ake yiwa wasu daga cikinsu.

Idan za’a iya tunawa aranar Lahadin da ta gabata ne, rundunar ‘yan sanda ta kasa ta bayar da sanarwar gayyatar Shugaban majalisar  dattawa Bukola Saraki domin ya je gabanta ya amsa tuhuma kan batun fashin da aka yi a Offa jihar Kwara.

Yayin daga daga bisani rundunar ‘yan sanda ta yi amai ta lashe, inda tace, tana bukatar Sarakin yayi mata bayani a rubuce ba sai ya zo da kansa ba.

Ya zuwa yanzu babu wani martani daga bangaren Gwamnati kan wannan batu, da kuma sanarwar da Kawu Baraje ya fitar ba.

LEAVE A REPLY