Daga Hagu zuwa dama, Shugaban jam'iyyar APC na kasa John Odigie-Oyegun sai Shugaban kasa Muhammadu Buhari sai mataimakinsa Yemi Osibanjo sai Shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki sai Sakataren jam'iyyar Mai-Mala Buni

Jagoran jam’iyyar APC na kasa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu bai halarci babban taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC ba da aka gudanar a ranar litinin.

DAILY NIGERIAN ta tabbatar da cewar Bola Tinubu wanda shi ne yake jagorantar kwamitin da yake sasanta ‘ya ‘yan jam’iyyar da basa ga maciji da juna, wanda aka ruwaito Tinubu din yana zaman doya da manja da Shugaban jam’iyyar John Oyegun.

amma kuma Shugaban kasa Muhammadu Buhari da Gwamnonin APC da Shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki da sauran mambobin majalisun dokoki na tarayya duk sun halarta.

“Wannan wani taron masu ruwa da tsaki ne da yake da matukar muhimmanci ace kowa ya halarta” Inji Sakataren yada labarai na jam’iyyar Bolaji Abdullahi, lokacin da yake shaidawa manema labarai.

“Idan zaku iya tunawa bayan babban taron masu ruwa da tsakin da aka yi a watan da ya gabata, Na shaida muku cewar. akwai wasu muhimman batutuwa guda biyu da ba’a tattauna su ba, domin ana bukatar karin lokaci domin nazartarsu”

“Wadannan su ne batun kwaskwarin ga kundin tsarin mulkin jam’iyyar  APC da kuma kwamitin da zai gabatar da rahoto kan tsarin tarayya”

“Wadannan wasu muhimman batutuwa ne da suke kan ajandar taron, a zaman da dattawan jam’iyyar zasu kuma yi gobe”

DAILY NIGERIAN ta ruwaito cewar Jam’iyyar  APC a taronta na watan fabrairu, an cimma yarjejeniyar karawa Shugaban jam’iyyar John Oyegun wa’adin shekara guda domin cigaba da jan ragamar jam’iyyar.

Shugaban jam’iyyar John Oyegun ya bayyana cewar an dauki wannan mataki ne da kyakkyawar niyya, yace wasu daga cikin ‘ya ‘yan jam’iyyar da abin bai yi musu dadi ba sun kai jam’iyyar kara kotu.

NAN

LEAVE A REPLY