Shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki lokacin da yake ganawa da manema labarai a harabar asibitin kasa dake Abuja, bayan da ya jagoranci 'yan majalisar domin yin dubiya ga Sanata Dino Melaye

Tawagar ‘yan majalisar dattawa, karkashin jagorancin Shugaban majalisar Abubakar Bukola Saraki, sun kaiwa Sanata Dino Melaye ziyarar dubiya a babban asibitin kasa dake Abuja, domin jajanta masa abinda ya faru da shi na fadowa da yayi daga mota inda ya samu raunuka.

A ranar Litinin aka tsare Sanata Dino Melaye a filin sauka da tashin jiragen saman kasa dake Abuja akan hanyarsa ta zuwa kasar Moroko domin yin wani aiki na musamman da Gwamnatin tarayya ta tura shi.

 

LEAVE A REPLY