'Yan Najeriya da aka kubuto da su daga Libiya sun dawo gida

Biyo bayan umarnin da Shugaban kasa ya bayar, Gwamnatin tarayya ta tashi wata kakkarfar tawaga domin zuwa Libiya su kubutar da ‘yan Najeriya daga cikin halin kangi da suke ciki, ya zuwa ranar Lahadin da ta gabata, kimanin mutane 481 ‘yan Najeriya dake watangaririya a Libiya aka ci nasararkubutar da su.

Anasa ran, dawo da ‘yan Najeriya kimanin 4,511 daga kasar Libiya nan ba da jimawa ba.

Dukkan wadan da aka dawo da su gida Najeriya, za’a killace su na wanni dan lokaci a Fatakwal,kafin mayar da su garuruwansu na asali.

A lokacin da suke nuna murnarsu da farinciki bayan dawowa gida, mutanan da aka kubutar da su sun samu rakiyar Babban Darakta Janar a hukumar bayar da agajin gaggawa ta NEMA Mista Mustapha Maihaja, tare kuma da mai baiwa Shugaban kasa shawara na musamman akan ‘yan Najeriya dake kasashen waje, Abike Dabiri-Erewa, tare kuma da rakiyar wakilan mai baiwa SHugaban kasa shawara ta fuskar tsaron kasa.

Tawagar wadda ta isa kasar Libiya karkashin jagorancin Ministan harkokin wajen Najeriya Mista Geoffrey Onyeama sun cimma matsaya tare da hukumomin kasar Libiya domin maido da ‘yan najeriya dake kasar gida a wata yarjejejniya da suka sanyawa hannu.

‘Yan Najeriyar da aka dawo da su gida, sun sauka a babban filin sauka da tashin jiragen sama na birnin Fatakwal da misalin karfe 5:05 na yamma, a lokacin da suka samu tarba daga Ministan harkokin wajen Najeriya dake filin jirgin saman yana jiran isowarsu.

A lokacin da yake jawabi bayan dawowarsu, Minnistan harkokin wajen Najeriya, Onyama ya ce “Amadadin Gwamnatin Najeriya da kuma SHugaban kasa, Ina yi muku barka da dawowa gida. Shugaban kasa tare da sauran al’ummar Najeriya na ta zumudi da fatan ganin kun dawo gida lafiya, Shugaban kasa ya bayar da duk abinda ake bukata domin tabbatar da kun dawo gida Najeriya cikin aminci”

“Mun je munga yaddada yawa daga cikinku suke cikin hali na tagayyara da kunci da kuma kangi”

“Mun samu fahimtar juna da hukumomin kasar Libiya, a sabida haka muna cike da farin cikin dawo da ku gida najeriya lafiya, a sabida haka, Gwamnati zata yi dukkan abinda ya dace domin mayar da ku jihohinku na asali nan ba da jimawa ba”

“A sabida haka,hakkin wannan Gwamnati ne kula da ‘yan Najeriya a ko ina suke a fadin duniya ba Najeriya kadai ba”

“Da yawanku mun sani an kaiku wadannan gurare ba tare da zabinku ba, wasu an yi musu karya da romn baka, aka gaya musu abinda ba gaskiya bane, to, ku sani, Gwamnatin Najeriya ba zata yasar da ku ba”

“Muna nan muna tattaunawa da Gwamnatocin jihohinku domin ganin yadda zasu zo su karbeku domin mika ku zuwa ga iyalanku”

Daya daga cikin ‘yan tawagar, Abike Dabiri-Erewa yace “Ba zamu taba yin kasa a guiwa ba wajen dawo da dukkan ‘yan Najeriya dake cikin kangi a Libiya.”

LEAVE A REPLY