Zauren majalisar wakilai ta tarayya

An samu rashin fahimtar juna, kuma an tashi baran baram a zaurane majalisar wakilai ta kasa a ranar Laraba, yayin da ake tattaunawa akan doka ta 006 a 2018 ta musamman da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanya mata hannu.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya, NAN, ya ruwaito cewar a ranar 5 ga watan Yuli Shugaban kasa ya sanyawa dokar hannu, inda dokar ta bukaci bincikar dukkan wanda ya mallaki kadarori da kuma bibiyar shiga da fitar  kudadensa.

Shugaba buhariya bayyana cewar ya zabi sanyawa dokar hannu saboda bukatargaggawa da ake da shi domin yin hakan, domin hana miyagun mutane taba kayan da suka mallaka ta haramtacciiyar hanya.

 

LEAVE A REPLY