Rundunar sojojin Najeriya masu atisayen AYEM AKPATUMA a ranar Asabar sun ci nasarar kama wasu matasa dauke da makamai a Takum, jihar Taraba.

Jaridar DAILY NIGERIAN ta ruwaito cewar tsohon Ministan tsaro na tarayyar najeriya, Theophillus Yakubu Danjuma a ranar Asabar, inda yayi kira ga al’ummar jihar Taraba da su tashi tsaye domin kare kansu daga hare haren makya sabida gazawar gwamnati.

Janar TY Danjuma, wanda dan asakin kabilar Takum ne, ya bayar da wannan gargadi a ranar Asabar a bikin yaye daliban jami’ar jihar Taraba a birnin Jalingo shalkwatar jihar.

“Dole ne ku tashi domin baiwa kanku kariya daga wadannan mutanen, idan kuka dogara ga jami’an tsaro domin su baku kariya, to dukkanku zaku mutu ne kuna neman taimako. Wadannan kashe kashe da ake yi a jihar Taraba dole ne su tsaya” A cewar Danjuma.

Sai dai a wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar sojin Najeriya, Texas Chukwu ya bayyana a ranar Lahadi cewar sun kama daya daga cikin masu dauke da makaman mai suna Rapheal Yakwa, lokacin da yake dauke dauke hotunan a sansanin sojin Najeriya dake jihar.

“Binciken farko farko sun nuna cewar, mutanan da aka kama suna daga cikin wasu mutane da wani mutum a jihar Taraba ya dauki nauyinsu domin haifar da yamutsi a yankin”

“Sannan kuma Yakwa ya tabbatar da cewar da hannunsa a duk wasu hare hare da aka kai jihar inda aka kashe mutane masu yawan gaske, ya kuma tabbatar da hakan ne ta hanyar bayar da wayarsa inda aka samu bayanai na sirri”

“Sakamakon bayanan da Yakwa ya bayar ne aka ci nasarar kama wani mai suna Irambariye Mamman wanda shi ne Shugaban matasan yankin da suke dauke da makamai domin tayar da tarzoma”

“Haka kuma, rundunar ta ci nasarar kama Micah Audu wanda ya bayyana cewar shi ma dan kungiyar ne” A cewar Chukwu.

LEAVE A REPLY