Akalla sojoji 23 ne daga rundunar sojin kasa ta Najeriya aka bayar da rahotannin bacewarsu tare da manyan motocin yaki guda takwas a wani artabu da rundunar sojan suka yi da ‘ya ‘yan kungiyar Boko Haram a yankin karamar hukumar Bama dake jihar Borno.

Ko sama ko kasa an nemi soja 23 an rasa, yayin da motocin yaki masu sulke guda 8 suma suka yi batan dabo, lokacin da ‘yan kungiyar  ta Boko Haram suka yiwa rundunar sojan kwanton bauna.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya, NAN, ya habarto cewar sashin bincike da kuma leken asiri na rundunar sojan ne ya tura wata bataliyar soja cikin motocin sulke guda 11 domin kawar da ‘yan kungiyar ta Boko Haram da suka yiwa wani kauye kawanya.

An dai kyautata zaton ‘yan kungiyar su ne wadan da suka arce daga dajin Sambisa zuwa yankin tafkin Chadi, inda suka silalo suka yiwa soja kwanton bauna.

 

LEAVE A REPLY