Jirgin saman sojan Najeriya mai suna Alpha Mi-35 ya kaddamar da wani hari ta sama a garuruwan Yanwari da mashema a jihar Zamfara inda suka kashe ;yan bindiga 20 dake tayar da zaune tsaye a yankin.

Jirgin dai ya kai wannan hari ne a wani sumame da suka mai suna da ‘Dirar mikiya’ suka samu nasarar halaka mutane ashirin daga cikin masu tayar da kayar baya a yankin.

A cewar rundunar sojan sama ta Najeriya, a wata sanarwa da suka fitar a ranar juma’a sun bayyana cewar suna yin aiki ne tare da rundunar sojan kasa domin samun nasarar farma ‘yan bindigar da suka addabi jihar ta Zamfara.

An kaddamar da wannan gagarumin farmaki ne a yankunan jihar Zamfara masu fama da tashin hankalin masu kai hare hare na babu gaira babu dalili a jihar.

LEAVE A REPLY