Siyasar Kano ta dauki wani sabon salo a ranar Asabar din nan, bayan da tsaffin Gwamnonin Kano Malam Ibrahim Shekarau da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso wanda suka jima suna adawa da juna sun gana a Aranar Asabar da daddare a gidan Malam Shekarau dake Abuja domin tattaunawa akan makomar siyasar Kano yayin da ake tunkarar shekarar zabe ta 2019.

Wannan dai shi ne haduwa ta farko da aka yi tsakanin tsaffin Gwamnonin guda biyun tun bayan da Sanata Kwankwaso ya dawo cikin jam’iyyar PDP a makon da ya gabata.

Idan ba’a manta ba a shekarar 2003 ne Malam Ibrahim Shekarau ya kayarda Gwamnan Kano na lokacin mai ci Rabiu Musa Kwankwaso.

Rahotannai sun bayyana cewar an yi wata takaitacciyar tattaunawa ta sirri tsakanin tsaffin Gwamnonin Kanon guda biyu.

Zamu kawo muku cikakken bayani nan gaba.

 

LEAVE A REPLY