Shugaban kasa Muhammadu Buhari tare da Gwamnan Jigawa Badaru Abubakar, yayin da Shugaban ya ziyarci jihar Jigawa a yau 14 ga watan Mayu 2018

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a yau litinin ya kai ziyarar yini biyu a jihar Jigawa inda zai kaddamar da wasu manya manyan ayyukan raya kasa da bunkasa harkar noma da Gwamnatin jihar karkashin Gwamna Badaru Abubakar ta aiwatar.

Ana sa ran Shugaba Buhari zai kaddamar da aikin noman rani na zunzurutun kudi Naira biliyan tara a Hadejia dake jihar ta jigawa. Bayan nan kuma ana sa ran Shugaban zai kaddamar da ayyukan tituna da asibitoci da sauransu a yayin wannan ziyara tasa ta yini biyu.

 

LEAVE A REPLY