Shugaban jam'iyyar APC na kasa mai barin gado, John Oyegun

Daga Hassan Y.A. Malik

Tsohon ministan man fetur a zamanin mulkin Sani Abacha, Cif Don Etiebet ne akan gaban cikin mutanen da ke neman zama shugaban jam’iyyar APC bayan da Shugaba Buhari da gwamnonin jam’iyyar suka ki amincewa da ci gaba da jagorancin jam’iyyar a karkashin Cif John Odigie-Oyegun.

Wannan kuwa ya biyo bayan wani zaman sirri da gwamnonin jam’iyyar ta APC suka yi ne a karshen makon da ya gabata don tattauna batun samar da magaji ga shugaba mai barin gado, Oyegun kamar yadda wata majiya mai tushe ta bayyana jiya Lahadi a Abuja.

Majiyar ta ci gaba da cewa, dalilin da ya sanya gwamnoni APC suka fi karkata ra’ayinsu ga Cif Etiebet shi ne saboda kyakkyawar alakarsa da Shugaba Muhammadu Buhari da kuma kokarin da jam’iyyar ta APC ke yi na kwato jihar Akwa Ibom a zaben 2019.

Gwamnonin sun janye goyon bayansu ga Adams Oshiomhole (tsohon gwamnan jihar Edo) sakamakon tsamar da ke tsakaninsa da wasu jiga-jigai a jam’iyyar, wanda hakan na iya jefa jam’iyyar cikin rikicin cikin gida.

Shi ma Rotimi Amaechi ya rasa goyon gwamnonin na APC sakamakon rashin karfin da jam’iyyar ba ta da shi a jiharsa ta Rivers, dalilin da ya sanya ya kasa kawowa APC bantenta a zaben 2015.

A yau, Litinin ne dai a ke sa ran jam’iyyar ta APC za ta yi wani babban taron shugabannin jam’iyyar na kasa da na jiha don yanke hukuncin batun tsawaita wa’adin mulkin shugabancin jam’iyyar a karkashin Cif Oyegun.

Shi dai Cif Don Etiebet ya taba rike mukamin shugaban jam’iyyar ANPP a shekarar 2003, a lokacin da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi wa jam’iyyar takarar shugaban kasa, inda Cif Obasanjo ya kayar da shi a babban zabe.

LEAVE A REPLY