Shugaban hukumar kula da shige da fice ta Najeriya Muhammadu Babandede ya...

Shugaban hukumar kula da shige da fice ta Najeriya Muhammadu Babandede ya halarci taron APC ta jihar Jigawa

Shugaban hukumar kula da shige da fice ta Najeriya, Muhammadu Babandedde, yana daya daga cikin wadanda suka halarci taron uwar jam’iyyar APC ta jihar Jigawa, a wani taron masu ruwa da tsaki da jam’iyyar ta gudanar a otal din African Continental dake Kaduna a ranar Asabar.

Mohammed Babandede

Muhammadu Babandede an nada shi a matsayin Shugaban hukumar kula da shige da fice ta Najeriya, bayan da Shugaba Muhammadu Buhari ya bayar da sanarwar sauke Martin Abeshi daga mukamin a watan Mayun 2016.

Wata majiya mai tushe tace, Babandede wanda yake dan asalin karamar hukumar Hadejia ta jihar Jigawa, ance yana shin shinan kujerar Sanata mai wakiltar Arewa maso gabashin jihar Jigawa a majalisar dattawa ta kasa.

A tsarin dokar jami’ai masu kayan Sarki a Najeriya ya hana masu sanye da kayan Sarki shiga sha’anin Siyasar jam’iyya.

DAILY NIGERIAN ta tabbatar da cewar, Babandede na daga cikin wadan da suka kadaa kuri’ar amincewa da Gwamnatin Gwamna Badaru Abubakar na jihar Jigawa.

Taron wanda aka yi shi na masu ruwa da tsaki na jihar Jigawa ya samu halartar Gwamnan jihar Muhammadu Badaru Abubakar da mataimakinsa Ibrahim Hassan Hadejiya da kakakin majalisar dokokin jihar Jigawa Isa Gwaram da kuma Sanatoci guda biyu Sanata Abdullahi Gumel da Sabo Nakudu.

Sauran su ne jagoran jam’iyyar APC a jihar Farouk Adamu Aliyu da Bello Mai-Sudan da Isa Gerawa da Ali Magashi da Sanata Danladi Sankara.

Taron wanda Shugaban jam’iyyar APC na jihar Ado Sani Kiri ya jagoranta, kuma mambobin jam’iyyar daga tarayya da jihar jigawa duk sun samu halartar taron.

A wata sanarwa da mai taimakawa Gwamna Badaru kan al’amuran yada labarai Auwal Sankara yace, Shugabannin jam’iyyar sun tattauna muhmman batutuwa,musamman halin da jam’iyyar take ciki a halin yanzu a jihar.

“Manyan jagororin jam’iyyar na jihar sun jinjinawa gwamna Badaru Abubakar akan irin yadda yake kokarin aiwatar da ayyukan cigaba a jihar, da kuma yadda tattalin arzikinjihar ke samun habaka a wannan mawuyacin lokaci”

“Jagororin sunkuma tabbatarwa da Gwamna Badaru da cikakken goyon bayansu, sanna kuma suka bukaci da ya jajirce wajen cika alkawuran da aka daukarwa al’ummar jihar a lokacin yakin neman zaben da ya gabata”

DAILY NIGERIAN ta kasa samun mai magana da yawun hukumar kula da shige da fice ta Najeriya Sunday James a lokacin da take hada wannan rahoto domin neman karin bayani.

LEAVE A REPLY

%d bloggers like this: