Shugaba Muhammadu Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mayarwa da tsohon shugaban kasa Dr. Goodluck Ebele Jonathan martini bayan da tsohon shugaban kasar yace gwamnatin Buhari ta kasa cikawa yan najeriya alkawarurrukan datayi musu lokacin yakin neman zabe.

Shugaban kasar ya mayar da martanin ne ta bakin mai Magana da yawunsa ta kafafen yada labarai, Mista Femi Adesina a shafinsa na twitter, inda yace zargin da jonathan yakeyi bashi da tushe ballantana makama.

Jonathan dai yace shekara biyu kenan amma har yanzu babu wani abu da gwamnatin APC tayi kuma har yanzu ana cigaba da gayawa yan najeriya karya da kuma jita-jita marasa tushe.

Tsohon shugaban ya bayyana hakane a jiya juma’a a ofishinsa dake Abuja lokacin da yakarbi bakwancin tsohon minister a gwamnatinsa kuma dan takarar shugaban cin jam’iyyar PDP, farfesa Tunde Adeniran.

Yaci gaba da cewa wadanda suka soki gwamnatinsa akan yabar litar man fetur akan naira 87 yanzu sunyi shiru duk da cewa yanzu yan najeriya suna siyan litar akan naira 145.

“Lokacin da gangar man fetur take dala saba’in da wani abu mun rage kudin mai yakoma naira 87 amma kuma yanzu gashi ana siyar da gangar mai akan dala 53 kuma yan najeriya suna siyan lita daya akan naira 143 kuma wadanda suke sukarmu a wancan lokaci yanzu sunyi shiru kuma suna ganin yadda abubuwa suke tafiya” inji Adesina

Sai dai mista Adesina ya bayyana cewa gaskiya ce ta banbanta tsakanin gwamnatocin biyu ba kamar yadda jonatahan din ya fad aba.

Kamar yadda Adesina ya bayyana, lokacin da aka kara kudin mai yakoma naira 145 yan Najeriya sunyi hakuri saboda sun yarda da gwamnatin shugaba Buhari.

Yaci gaba da cewa yan Najeriya sunyi zanga zanga ne a lokacin jonathan bayan Ankara kudin mai saboda basu yarda da kamun ludayin gwamnatin ta PDP ba.

A karshe yaci banbancin a bayyane yake  kuma kowa yasan gaskiya

LEAVE A REPLY