Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya karbi bakuncin Shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta a fadar White House dake birnin Washington a gundumar Kwalambiya.

Shugaba Kenyatta ya bayyana a shafinsa na Facebook cewar yana kasar ta Amurka je domin amsa gayyatar da Shugaban Donald Trump ya yi masa a wata ziyara ta gajeran lokaci.

Shugaba Trump da takwaransa na Kenya dai zasu yi tattaunawa ne akan Abinda ya shafi kasashen biyu da kuma batutuwan da suka shafi harkokin diplomasiyya.

Idan ba a manta ba a jiya aka ruwaito Shugaban Amurka Trump na caccakar Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, inda ya bayyana cewar sam bai ji dadin haduwa da shi ba, a cewarsa Shugaba Buhari Naisa koshin lafiya.

LEAVE A REPLY