Yayin da Sarki Muhammad na Moroko ya ke zagaya da Shugaba Buhari a babban birnin kasar Rabat

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya samu kyakkyawar tarba a yayin ziyarar yini biyu da ya kai kasar Moroko a jiya Lahadin. Sarkin kasar Muhammad na shida shi ne ya marabci Shugaban kasa Muhammadu Buhari tare da shirye masa jerin gwanon motoci na kasaita.

Tun farko dai, Shugaba Buhari ya karbi faretin ban girma da akai masa a fadar Sarkin dake babban birnin kasar Rabat. Daga bisani aka wuce kai tsaye da Shugaba Buhari tare da mai masaukinsa Sarki Muhammad zuwa wani kayataccen wajen da aka shiryawa Shugaba Buhari liyafar bangirma.

Shugabannin biyu dai sun amince su yi aiki tare tsakanin Najeriya da Moroko wajen harkokin diplomaciyya da kuma cinikayya a tsakaninsu. Haka kuma, sun amince su yi aiki kafada da kafada ta fannin ayyukan noma da gina hanyoyi da ayyukan ma’adanai.

Bayan haka kuma, Najeriya da Moroko sun amince su shimfida bututun iskar gaz daga yankin Kudu masu kudancin Najeriya zuwa cikin kasar ta Moroko, aikin dai zai keta saharar kasar ya nausa sosai.

 

LEAVE A REPLY