Yayin da Shigaban kasa Muhammadu Buhari yake sanya hannu akan kasa kudin shekarar 2918

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Laraba 20 ga watan Yuni ya rattaba hannu kan kasafin kudin shekarar 2018. Sanya wannan hannu da Shugaba Muhammadu Buhari yayi, hakan ya nuna kasafin kudin ya zama doka kuma zai fara aiki ba da bata lokaci ba.

An dai kai ruwa rana tsakanin fadar Shugaban kasa da kuma ‘yan majalisun dokoki na tarayya kan wannan batun kasafin kudin shekarar 2018. Inda ko a lokacin da majalisar ta mikawa Shugaban kasa kwafin kundin kasafin da suka tace suka tsefe, sun bayyana cewar sun yi karin kudin da suka kai naira biliyan 5 a cikin kasafin kudin.

Sai dai kuma, Shugaba Buhari a jawabansa yayin da yake sanya hannu a kasafin kudin, ya zargi ‘yan majalisun dokokin da yin cushen abinda suka ga dama a cikin kasafin kudin, kamar dai yadda aka sha kwarbai a kasafin kudin shekarar 2017 inda dan majalisa Jibrin Kofa ya tona asirin cushen da majalisun suka yi a cikin kasafin kudin.

 

LEAVE A REPLY