Shugaban kasa Muhammadu Buhari tare da Gwamnan jihar Borno Kashim Shettima

Gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima a yau da safe ya bayar da sanarwar wata ziyara da Shugaban tarayyar Najeriya Muhammadu Buhari ya kai jihar a yau da safe, akan hanyarsa ta zuwa jihar Yobe domin ganawa da iyayan ‘yan matan makarantar Dapchi da aka sace.

Wannan ita ce ziyarar farko da Shugaba Muhammadu Buhari ya kai jihar Yobe tun bayan zabesa a matsayin Shugaban kasa shekaru uku da suka wuce.

Shugaba buhari dai ya yanke shawarar kai wannan ziyara ne bayan da ya sha suka kan batun sace ‘yan matan da ‘yan kungiyar Boko Haram suka yi a Dapchi.

LEAVE A REPLY