Daga Hassan Y.A. Malik

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi shirin tafiya birnin London da ke kasar Burtaniya a ranar Litinin mai zuwa, kamar yadda wata majiya daga fadar gwamnatin tarayya ta bayyana.

Majiyar wacce ta roki da kar a bayyan sunanta ta kara da cewa tafiyar za ta baiwa shugaban damar yin wasu lamuran da suka shafe shi, ma’ana ziyarar ba ta aiki ba ce.

Sai dai kuma majiyar ba ta yi karin bayani ba game da wadannan abubuwa da shugaban zai je yi.

Wannan ziyara dai za ta zo ne dab da lokacin da za a yi taron shugabannin kasashen da ke kungiyar Commonwealth (CHOGM), a birnin London tsakanin 15 zuwa 20 ga watan nan.

Da aka tuntubi mai taimaka wa shugaban a harkokin yada labarai, Malam Garba shehu, bai yi karin haske ba game da ziyarar.

A shekarar da ta gabata dai Shugaba Buhari ya shafe tsawon watanni ya na jinya a Birnin London, inda dadewar ta shi ta haifar da cecekuce a fadin kasar nan, har ta kai wasu na bukatar ya sauka daga kujerar shi idan ya gaza.

LEAVE A REPLY