Daga Hassan Y.A. Malik

A yau Talata ne Shugaba Muhammadu Buhari zai bar Najeriya zuwa birnin Landan na kasar Burtaniya.

Fadar shugaban kasa ce ta fitar da wata sanarwa akan wannan balaguro na shugaban kasa da zai shafe kwanaki hudu a can Landan din.

Sanarwar ta bayyana cewa ganawa tsakanin shugaba Buhari da likitansa ya biyo bayan tsayawa da jirgin shugaba Buhari ya yi a Burtaniya a makon da ya gabata bayan ya bar Amurka.

Dakatawar ta ba-zato-ba tsammani da Shugaba Buhari ya yi a Burtaniya na da alaka da ‘yar matasala da jirginsa ya samu, wanda hakan ya sanya dole aka tsaya don duba lafiyar jirgin, wannan tsayawa da aka yi ya sanya shugaba Buhari ya gana da likitansa, inda har likitan ya bashi lokaci ya zo ya duba lafiyarsa.

Buhari zai dawo gida Nijeriya a ranar 12 ga watan Mayu, 2018, inda da ya dawo zai kai ziyarar aiki na kwanaki biyu a ranekun Litinin da Talata 15 da 16 ga watan Mayu, 2018 a jihar Jigawa.

 

LEAVE A REPLY