Shugaba Buhari da takwaransa na kasar Ghana Nana Akufo Addo

Shugaba Muhammadu Buhari a ranar litinin dinnan, zai bar Najeriya zuwa birnin Accra na kasar Ghana domin halartar bikin cikar kasar Shekaru 61 da samun mulkin kai,wanda za’a yi a ranar Talata.

Mai taimakawa Shugaban kasa kan hulda da kafafen yada labarai, Miista Femi Adeshina, shi ne ya bayyana hakan a ranar lahadi a birnin tarayya Abuja.

A cewar sanarwar, Shugaba Buhari shi ne kadai wani Shugaban kasar da aka gayyata wajen wannan biki a matsayin babban bako na musamman.

“Haka kuma,bayan kasancewarsa babban bako, Shugaba Buhari shi ne kadai wani Shugaban da aka tsara zai yi jawabi a yayin wannan babban taro mai dumbin tarihi”

Bayan haka kuma, Shugaba Buhari zai yi amfani da wannan damar domin dinkin wata daddadiyar baraka tsakanin mutanan Ghana da na Najeriya kan kallon hadarin kaji da ake yiwa juna.

Haka kuma, sanarwar ta kara da cewar, Shugaban kasa zai samu rakiyar ministan harkokin wajen Najeriya, Geoffrey Onyeama da mai baiwa Gwamnati shawara ta fuskar tsaro Babagana Munguno, kuma ana sa ran dawowarsu Abuja a ranar Talata.

NAN

LEAVE A REPLY