Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi wata ganawar sirri da Shugaban jam’iyyar APC John Odigie-Oyegun ranar juma’a a Abuja.

Wannan ganawa ta Shugaba Buhari da Shugaban jam’iyyar APC na kasa, tana zuwa ne sa’o’i 24 bayan da jagoran jam’iyyar APC na kasa Bola Ahmed Tinubu ya zargi Mista Pyegun da yiwa shirinsa na sasanta ‘ya ‘yan jam’iyyar kafar ungulu.

Shugaban jam’iyyar ta APC wanda ya isa fadar Shugaban kasa da misalin karfe 3 na rana, ya fito daga ganawar sirrin da yayi da Shugaban kasa Muhammadu Buhari da misalin karfe 3:50 ba tare da yayi magana da ‘yan jarida ba.

Sai dai kuma, DAILY NIGERIAN ta samu tabbacin cewar Shugaban jam’iyyar na kasa ya nemi ganawa da Shugaba Buhari ne domin fayyace masa gaskiyar abinda ke faruwa dangane da zarge zarge da Bola Ahmed Tinubu yayi masa kan kokarin yin kafar ungulu kan shirinsa na sasanta ‘ya ‘yan jam’iyyar da basa ga miciji da juna.

A cikin wasikar da Mista Tinubu ya rubuta mai shafi 8, wadda kuma ya aikewa Shugaba Muhammadu Buhari da Shugaban majalisar dattawa da kakakin majalisar dokoki ta kasa Yakubu Dogara ya a ranar 21 ga watan Fabrairun nan, ya zargi Mista Oyegun da bata al’amura a kokarin Tinubun na sasanta rikicin APC.

Mista Tinubu a cikinwasikar tasa ya bayyana yadda Shugaban jam’iyyar Mista Oyegun yake ta kokarin ganin ya tadiye yunkurin Tinubu din na samun nasarar sasanta ‘ya ‘yan jam’iyyar ta APC tare da sabauta shirin.

Sai dai har ya zuwa lokacin hada wannan rahoto Mista Oyegun bai ce komai ba dangane da wannan zarge zarge da ake yi masa na kawo tsaiko a kokarin sasanta rikita rikitar da ta dabaibaye jam’iyyar ta APC a kusan dukkan jihohi.

LEAVE A REPLY