Shugaba Muhammadu Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari ya yi fatali da dikar sake fasalin zaben kasarnan wanda majalisar dattawa ta yi, inda aka bambanta zaben Shugaban kasa da na ‘yan majalisar dattawa da wakilai, wanda dukkan ‘yan majalisun tarayya suka amince da sauya lokutan zabubbukan.

A cewar Shugaban kasa,akwai dalilai guda uku da suka sanyi shi yin fatali da batun sake fasalin dokokin zabubbukan dake tafe.

Shugaban ya bayyana kin amincewarsa da sake fasalin zabubbukan ne a wata wasika da ya aikewa Shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki da kuma takwaransa na majalisar wakilai Yakubu Dogara.

Ana sa ran dai Shugabannin majalisun biyu zasu karanta wasikar da Shugaban kasa ya aike musu tsakanin yau zuwa gobe.

Daman dai tuni kungiyoyi da lauyoyi suka nuna damuwa kan batun sake fasalin zabubbukan da majalisun tarayya suka yi,inda suka yi kira kada Shugaban kasa ya amince da batun.

 

LEAVE A REPLY