Shugaba Muhammadu Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya rubutawa majalisar dattawa wasikar neman amincewa da mutane 27 domin basu mukamai a ma’aikatun Gwamnati daban daban.

Shugaban majalisar dattawa, Sanata Bukola Saraki shi ne ya karanta wasikarda Shugaban kasa ya aikewa da majalisar, kafin dage cigaba da zaman majalisar zuwa mako mai zuwa.

A cewar wasikar farko da aka akaranta, Shugaban kasa yana neman majalisar dattawa ta amince da nadin Festus Okoye a matsayin kwamishinan tarayya a hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta INEC.

“A cewar wasikar, abisa dogaro da sashi na 154 karamin kashi na 1 na cikin kundin tsarin mulkin Najeriya, na 1999, Ina mai neman sahalewarku domin nadin Lauya Festus Okoye a matsayin kwamishinan tarayyar a hukumar zabe da zai wakilci yankin kudu maso gabas.

“Muna fatan majalisa zata mince da wannan nadi da muka yi, ina kuma yi muku fatan samun hadin kaina a ko da yaushe” A cewar wasikar ta Shugaban kasa.

A wata wasikar kuma da fadar ta shugaban kasa ta aikewa da Shugaban majalisar dattawa, Shugaban kasa Muhammadu Buhari na neman amincewar majalisar domin nada mutane 23 a matsayin mambobin hukumar kidaya ta kasa, tare kuma da amincewa daa nadin mutum biyu da ba lauyoyi ba da suka kunshi Abba Ali (Katsina, Arewa maso yamma) da kuma Mohammed Sagir (Niger, Arewa ta tsakiya).

Mutane 23 da za’a nada mambobin hukumar kidaya ta kasa su ne; Nwanne Johnny Nwabuisi (Abiya) da Dr Clifford Zirra (Adamawa) da Mista Chidi Christopher Ezeoke (Anambra) da Barrister Isa Audu Buratai (Borno) da kuma Charles Iyam Ogwa (Cross River).

Sauran su ne: Sa Richard Odibo (Delta) da Okereke Darlington Onaubuchi (Ebonyi) da Mista A.D. Olusegun Aiyajina (Edo) da Ejike Ezeh (Enugu) da Hon. Abubakar Mohammed Danburam (Gombe) da Prof. Uba S.F. Nnabue (Imo) da kuma Dr. Abdulmalik Mohammed Durunguwa (Kaduna).

Ragowar kuma su ne: Sulaiman Ismaila Lawal (Kano) da Prof. Jimoh Habibat Isah (Kogi) da Dr. Sa’adu Ayinla Alanamu (Kwara) da Nasir Isa kwarra (Nasarawa) da Barrister Aliyu Datti (Niger) da Yeye (Uwargida) Seyi Adererinokun Olusanya (Ogun).

Na karshen su ne: Yarima Oladiran Garvey Iyantan (Ondo) da Sanata Mudashiru Oyetunde Hussain (Osun) da Madam Cecilia Arsun Dapoet (Plateau) da Dr. Ipalibo Macdonald Harry (Rivers) sai kuma Sale S. Saany (Taraba).

LEAVE A REPLY