Shugaba Muhammadu Buhari
Daga Hassan Y.A. Malik
 

La’akari da shawarwarin da majalisar alkalai ta kasa,NJC, ta bayar, shugaba Muhammadu Buhari ya tabbatar da hukuncin ritayar dole ga Mai shari’a Adeniyi Ademola na babbar kotun gwamnatin tarayya da ke Abuja tare da yanke hukuncin sallama daga aiki ga Mai shari’a O.O. Tokode, na babbar kotun gwamnatin tarayya da ke Benin, jihar Edo.

Wannan hukunci ya yi daidai da tanadin sashe na 292 (1)(b) na shekerar 1999 na kundin tsarin mulkin Nijeriya, a cewar mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin yada labarai, Malam Garba Shehu.

Haka kuma, Mai shari’a O.O Tokode zai mayar wa da gwamnati dukkan albashin da ya karba ba bisa ka’ida ba tun daga ranar 2 ga watan Disamba, 2015, lokacin da aka tabbatar da shi a matsayin alkalin babban kotu na kasa.

Shugaba Muhammadu Buhari, ya yi kira ga alkalan kasar nan da su gabatar da aikinsu tsakaninsu da Allah tare da taimakawa gwamnati wajen yaki da cin hanci da rashawa.

LEAVE A REPLY