Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta bayar da sanarwar soke zaman majalisar zartarwa na wannan makon da aka saba gudanarwa duk mako.

A cewar wata sanarwa da femi Adesina ya fitar ranar litinin, ta bayyana cewar Gwamnati ta bayar da umarnin soke zaman majalisar zartarwa na wannan makon.

Shugaba Buhari ba zai samu damar halartar zaman bane sabida wasu muhimman ayyuka da suka shafi yankin tafkin Chadi da zai halarci wata tattaunawa ta musamman akai.

Mista Adeshina, wanda shi ne mai taimakawa Shugaban kasa na musamman kan hulda da kafafen yada labarai ya bayyana cewar, mafiya yawancin Ministocin Buhari zasu halarci wannan tattaunawa da za’a kan yankin tafkin Chadi a otal din Transcorp dake Abuja babban birnin tarayyar Najeriya.

 

LEAVE A REPLY