Shugaban kasa Muhammadu Buhari

Ana iya cewar ziyarar Shugaba Buhari zuwa kasar Amurka kwalliya ta biya kudin sabulu, domin ya ci nasarar dawo da miliyoyin dalolin da ‘yanNajeriya suka kwasa suka jibge a kasar Amurka.

An bayyana cewar kimanin dalar AMurka miliyan 500 Shugaba Buhari ya ci nasarar dawo da su lalitar Gwamnatin Najeriya, kimanin Naira biliyan 190. Wadannan nan dai wasu kudade ne da ake zaton wasu barayi a Najeriya sun sace sun jibge a bankunan Amurka.

Atoni Janar na Najeriya, kuma ministan Shari’ah Abubakar Malami, shi ne ya bayyanawa manema labarai a birni Washington DC cewar shi da Atoni janar na kasar Amurka zasu sake zama ranar Talata domin karkare batun dawo da kudaden najeriya da aka sace aka jibge a bankunan Amurka.

Malami yace ana bin lamarin cikin tsanaki tare da duban dama da hauni, dan ganin ba a ci karo da wani abu da ka iya zama tarnaki ba.

Ya cigaba da cewar “Mun cimma gagarumar nasara a yayin wannan ziyara zuwa Amurka inda muka bibiyi sawun wasu kudade da aka sata daga Najeriya aka kaisu Amurka” Acewar Malami.

LEAVE A REPLY