Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ziyarci rundunar sojan Najeriya dake jihar Zamfara tana yaki da miyagun mutane ziyarar bazata.

Shugaban ya kai wannan ziyara ne kafin ya tashi daga filin jirgin saman Umaru Musa YarAdua zuwa babban birnin tarayya Abuja.

A yayin wannan ziyara ta ba safai ba, Shugaba Buhari ya jinjinawa runudnar sojan da akaiwa lakabi Sharar Daji da kuma Dirar Mikiya.

Daga nan Shugaban ya bukaci rundunar sojan da su sake zage dantse wajen yin ayyuka dan nuna kishin Kasa da kuma kare muradunta.

LEAVE A REPLY