Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kai wata ziyarar bazata zuwa jihar Bauchi domin duba irin bala’in da kakkarfariska ta haifar a jihar da kuma jajantawa ‘yan kasuwar Azare da suka samu ibtila’in gobara a makon da ya gabata.

Da misalin karfe 9:30 na safiyar Alhamis din nan ne jirgin da yake dauke da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sauka a filin sauka da tashin jiragen saman Sa Abubakar Tafawa Balewa dake Bauchi.

Gwamnan jihar Bauchi Mohammed Abdullahi Abubakar tare da rufawar mukarraban Gwamnatinsa da kuma kakakin majalisar dokokin jihar Kawuwa ne suka tarbi Shugaba Buhari a fiilin jigin saman bauchin.

Shugaban huumar bayar da agajin gaggawa ta kasa NEMA, Alhaji Musa Maihaja tare da Sakataren Gwamnatin jihar Bauchi Nadada Umar na daga cikin wadan da suka tarbi Shagan kasa.

LEAVE A REPLY