Shugaba Muhammadu Buhari
Shugaba Muhammadu Buhari

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari yayi alkawarin sake jajircewa wajen samar da ayyukan yi da Gwamnatinsa ke kokarin samarwa dumbin matasan Najeriya.

Shugaban ya bayyana hakan nw wajen bikin kaddamar da kamfanin barasa mafi girma a Najeriya. Shugaban wanda Sakataren Gwamnatin tarayya Boss Guda Mustapha ya wakilta ya tabbatarwa da kamfanin Breweries mai samar da barasa tabbacin samun hadin kan gwamnatinsa wajen cimma manufofin kamfanin.

An kaddamar da wannan kamfani je a jihar Ogun dauke kudu maso yammacin Najeriya. Darajar kamfanin dai ya kai kimanin Dakar Amurka miliyan 250. Kuma zai kasance kamfanin barasa mafi girma a yammacin Afurka.

LEAVE A REPLY