Shugabankasa Muhammadu Buhari, ya jagoranci zaman majalisar zartarwa na farko a fadar Gwamnati dake Aso Roack Villa a Abuja a ranar Laraba.

A zaman dai an yi batun kasafin kudin Shekarar 2017 da ta gaba ne, a shirye shiryen Gwamnatin na fara yin manyan ayyukan raya kasa a sassan kasarnan a wannan sabuwar shekarar.

Jawabin da Shugaban kasa yayi na sabuwar Shekara kusan shi ne ke zaman ajanda ta farko a jadawalin abinda za’a tattauna a yayin wannan zama, kusan dukkan ministocin Gwamnatin Buhari sun halarci wannan zama.

A zaman da majalisar take yi duk sati a irin wannan rana, wannan shi ne zama na farko a sabuwar Shekarar 2018 duk da cewar majalisar Ministocin ta tafi hutun karshenshekara tun 20 ga watan Disambar da ya gabata.

LEAVE A REPLY