Shugaba Buhari a jihar Ekiti

SHugaban kasa Muhammadu Buhari ya isa jihar Ekiti domin gangamin yakin neman zaben jam’iyyar  APC a cigaba da yakin neman zaben Gwamnan jihar da za ai nan gaba a ranar 14 ga watan Yuli.

Shugaban na jihar ne domin nemawa dan takarar Gwamnan jihar na jam’iyyar APC Kayode Fayemi kuri’a yayin zaben Gwamnan da za ai.

Anyi wannan gangami ne na jam’iyyar APC a filin wasa na Oluyemi Kayode , wanda jiga jigan jam’iyyar na kasa suka halarta ciki kuwa harda Bola Tinubu da Bisi Akande da Segun Osoba da Sakataren Gwamnatin tarayya Boss Mustapha da ministan harkokin cikin gida Abdurrahman Danbazau da kuma Sanata Andy Uba.

 

 

A

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Haka kuma, gwamnan jihar Ekiti Ayodele Fayose ya gargadi dukkanin ‘yan jam’iyyarAPC da su fice daga jihar Ekiti da zarar sun kammala gangamin yakin neman zaben nasu, inda yace kara lokaci a jihar  zai janyo musu matsala.

LEAVE A REPLY