Shugaba Buhari tare da Sakataren harkokin wajen Amurka Rex Tillerson

Sakataren harkokin wajen Amurka, Rex Tillerson a ranar litinin ya bayyana gamsuwar da cewar ‘yan matana makarantar Dapchi da ‘yan kungiyar Boko Haram suka sace, za’a sake su cikin aminci tunda an fara tattaunawa domin ganin an sako su.

Mista Tillerson ya bayyana hakan ne a lokacin da yake magana gaban manema labarai, bayan sun yi wata ganawar sirri shi da Shugaba Muhammadu buhari a fadar Gwamnati dake Aso Villa a Abuja.

Sakataren harkokin wajen na Amurka, ya bayyana cewar a shirye gwamnatin kasar Amurka take domin baiwa Najeriya tallafi wajen ganin an sako wadannan ‘yan mata da aka sace da ma sauran ‘yan matan Chibok da har yanzu ba’a sako wasun su ba a hannun ‘yan kungiyar Boko Haram.

Ya bayyana cewar, Boko Haram ba wai kawai barana ce ga Najeriya kadai ba, har da sauran kasashen Afurka dake kudu da Sahara.

Daga bisani kuma, Tillerson ya yabawa Shugaba Muhammadu Buhari musamman kan yadda ya jagorancin kasashen yammacin Afurka wajen yaki da cin hanci da rashawa, wanda a cewarsa hakan ya janyowa Buharin martaba a kungiyar tarayyar Afurka ta AU.

LEAVE A REPLY