Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dawo babban birnin tarayya Abuja, bayan da ya shafe kwanaki uku a mahaifarsa dake Daura a wata ziyara da yaje ta musamman domin yin ta’aziyar Sanata Mustapha Bukar, Sanata mai wakiltar yankin Daura a majalisar dattawan najeriya, da Allah ya yiwa rasuwa a wannan makon mai karewa.

KAmfanin dillancin Labarai na Najeriya, NAN, yace jirgin da yake dauke da Shugaba Buhari ya bar filin sauka da tashin jiragen sama na Umaru Musa YarAdua dake Katsina, zuwa babban birnin tarayya tare da ‘yan rakiyarsa da misalin karfe 10 da minti 45 na safiyar nan.

Jirgin da yake dauke da Shugaban kasa ya sauka a Abuja da misalin karfe 11 da minti 28 na safiyar yau.

Shugaban ma’aikatan fadar Shugaban kasa, Malam Abba Kyari da Ministan babban birnin tarayya Abuja,Alhaji Muhammad Bello da sauran manyan jami’an tsaro da sauran masu taimakawa Shugaban kasa ne suka tarbe shi a filin jirgin samankasa dake Abuja.

A ranar Juma’a ne dai Shugaban kasa tare da Mai Martaba Sarkin Daura da sauran al’ummar Daura suka hadu domin yin adduar sadakar ukun Sanata Mustapha Bukar da Allah ya yiwa rasuwa.

LEAVE A REPLY