Daga Hassan Y.A. Malik

Shugaban Amurka, Donald Trump zai sauki takwaransa na Nijeriya, Muhammadu Buhari a fadar gwamnatin Amurkan da ke birnin Washington DC a ranar 30 ga watan nan na Afrilu.

Shugabannin biyu za su tattauna ne akan ‘Yaki da ta’addanci’ da kuma ‘Habaka tattalin arziki’.

Wata sanarwa da fadar shugaban kasar Amurka ta fitar a jiya Lahadi ta bayyana cewa, “Shugaba Trump zai gana da shugaban Nijeriya kan batun danganta tsakanin Nijeriya da kasar Burtaniya da kuma Fira ministar Burtaniya Theresa May da kuma yadda kasashen da shugabannin za su yi aiki tare wajen fitar da dabarun yadda za a fuskanci yaki da ta’addancin da kuma yadda za a habaka tattalin arziki da kuma yadda za a dikile duk wani abu da ke kokarin kawowa dimokuradiyya tarnaki a kokarin dawowa da Nijeriya matsayinta na jagoranci a nahiyar Afirka.”

Shugaba Buhari, a ranar Larabar da ta gabata, ya gana da babban limamin darikar Angalika, Archbishop na Canterbury, Justin Welby a London.

LEAVE A REPLY