Shugaban kasa Muhammadu Buhari a yayin yakin neman zaben shekara ta 2015

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya bayyana aniyarsa ta sake tsayawa zabe a kakar zabe ta shekarar 2019. Shugaban ya bayyana hakan ne a Abuja waten taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC.

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufai, ya bayyana hakan a ranar Litinin a shafinsa na facebook.

Haka kuma, mai yiwa Shugaban kasa hidima na musamman Bashir Ahmad ya tabbatar da hakan a shafinsa na Twitter,inda yace Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayyana aniyarsa ta sake tsayawa zabe a shekarar 2019.

Zamu saurari karin bayani idan anjima.

 

 

LEAVE A REPLY