Shugaban kasa Muhammadu Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya amince da sanya ranar 12 ga watan Yunin 1993 a matsayin ranar tunawa da demokaradiyya ta Gwamnatin Najeriya.

A wata wasika da aka wallafa a shafin Twitter na Shugaban kasa a ranar Laraba, Shugaban ya bayyana dalilin da suka sanya aka ayyana ranar a matsayin ranar tunawa da demokaradiyya.

“Tun kusan shekaru goma sha takwas da suka gabata, ‘yan najeriya na murnar ranar 29 ga watan Mayu a matsayin ranar tunawa da demokaradiyya a Najeriya. Wannan ranar da ake murnar zagayowarta, ita ce rana ta biyu da aka samu musayar mulki daga Gwamnatin soja zuwa farar hula a tarihin Najeriya, tun bayan ranar 21 ga watan Oktoban 1979,inda a karon farko Gwamnatin soja ta mikawa farar hula mulkin kasarnan”

“Sai dai kua, bayan da muka saurari ra’ayin ‘yan Najeriya, wannan rana ta 12 ga watan Yuni 1993, ita ce ranar da ta fi dacewa da ranar tunawa da demokaradiyya a Najeriya. Tafi kama da ranar Demokaradiyya akan ranar 29 ga watan Mayu”

 

LEAVE A REPLY