Shugaba Muhammadu Buhari yayin da yake jagorantar zaman majalisar zartarwa na wannan makon

A yayin zaman majalisar zartarwa na yau Laraba, wanda Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranta a babban birnin tarayya Abuja. Shugaban ya amince a fitar da zunzurutun kudi Naira biliyan 185.2 domin giggina tare da gyara manyan hanyoyin Gwamnatin tarayya guda 14 a duk fadin Najeriya.

Mai taimakawa Shugaban kasa na musamman akan hulda da kafafen yada labarai Femi Adesina ne ya bayyanawa manema labarai hakan a fadar Shugaban kasa, bayan kammala zaman majalisar zartarwa na wannan makon da aka yi yau Laraba a fadar Shugaban kasa dake Aso Villa a Abuja.

Femi Adesina wanda yake tare da ministan lafiya Isaac Adewole da kuma ministan ciniki da masana’antu Okechukwu Enelamah ya bayyana ‘yan jaridu cewar, hanyoyin da zasu ci gajiyar wannan zunzurutun kudade suna jihohin Yibe da Adamawa da Binuwai da Kwara da Ekiti da Legas da Ogun da Edo da Enugu da Anambara da kuma Sakkwato.

Sannan kuma, ya lisafta hanyoyin kamar haka, Gwoza zuwa Dambuwa zuwa Goniri zuwa Ngamdu wadan da suke jihohin Borno da Yobe zasu lashe kudi Naira biliyan 34.608; sannan kuma sai hanyar Mayo Belwa zuwa Jada zuwa Ganye zuwa Torngo dukkansu a jihar Adamawa zasu lakume Naira biliyan 22.699 da kuma hanyar Ado zuwa Ifaki zuwa Otun duk a jihar Kwara zasu lakume Naira biliyan 6.

Ya cigaba da cewar Babbar gadar Mukurdi a jihar Binuwai za’a gyatta ta wanda zata lashe Naira biliyan 4.617, sai hanyar Ihugi zuwa Korinya zuwa Wase zuwa Ankor a jihar Ninuwai zasu lashe Naira biliyan 15.641 da kuma hanyar Gbagi zuwa Apa zuwa Owode a yankin Badagiri ta jihar Legas zasu lashe Naira biliyan 4.366.

Sauran hanyoyin sune, sake gina hanyar Ijebu zuwa Ita Egba Owonowen a jihohin Ogun da Oyo zasu lashe Naira biliyan 9.833, sannakuma za’a kashe Naira biliyan 7.506 domin aikin tagwaita hanyar Jattu zuwa Fugar zuwa Agenebode a jihar Edo.

Sannan kuma, akwai hanyar Mukrdi zuwa Gboko zuwa Wannune zuwa Yander a jihar Binuwai, za a sake gina hanyar akan Naira biliyan 18.669; sannan sai hanyar Enugu zuwa Fatakwal wadda zata lashe Naira biliyan 13.933.

Femi Adesina ya cigaba da cewar, za kuma a kashe  zunzurutun Naira biliyan 6.249, domin gina hanyoyin Umulung zuwa Umulunge zuwa Umoke da kuma Amokwu d Egde zuwa Opeyi zuwa Awhum.

LEAVE A REPLY