Shugaba Muhammadu Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari tare da rakiyar Shugaban hukumar Kwastan ta kasa Kanar Hameedu Ali mai ritaya zasu kai ziyara zuwa kasar Turkiyya nan gaba a wannan makon. Wannan ziyara dai ta biyo bayan wasu miyagun makamai da hukumar Kwastan ta kasa ta kama a tashar jiragen ruwa ta Najeriya dake Legas, wanda ake zargin anyi safarar su ne daga kasar Turkiyya.

Jami’in da ke kula da sashen bincike na hukumar kwastan ta kasa, Aminu Dangaladima, shi ne ya bayyanawa manema labarai wannan bayanin a karshen mako. A yayin wannan ziyara ana sa ran za’a tattauna akan batun shigo da makaman da aka yi najeriya daga kasar ta Turkiyya.

Haka nan, Dangaladima, ya kara da cewar, a yanzu haka, hukumarsu tana tsare da mutane da yawa akan batun shigo da wadannan kamai wanda yawansu yakai 2,671. Tuni dai dama shugaban hukumar ta Kwastan yake zargin ana shigo da makamai Najeriya daga kasar ta Turkiyya.

Koa watan satumbar da ya gabata, hukumar ta kwastan, ta kama wasu makamai da yawansu yakai 470,wadan da suma ake zargin daga kasar Turkiyya aka shigo da su zuwa Najeriya.

LEAVE A REPLY