Rahotanni daga fadar Shugaban kasa na tabbatar da cewar Shugaban kasa Muhammadu Buhari na yin wata ganawar sirri tsakaninsa da Gwamna Akinwunmi Ambode na jihar Legas.

Bayanai sun nuna cewar Ambode na yiwa Shugaba Muhammadu Buhari bayani je akan halin da jam’iyyar APC take ciki a jihar Legas tun bayan da rahotanni suka nuna cewar akwai baraka a jam’iyya reshen jihar Legas.

Bayan haka Gwamna Ambode yana shan matsin lamba na ya ajje kudurinsa na sake neman Gwamnan jihar Legas karo na biyu. Inda akai ya ruwaito bayanai na samun sabani tsakaninsa da mai gidansa kuma jagiran jam’iyyar APC na kasa Bola Ahmed Tinubu.

LEAVE A REPLY