Shugaba Buhari tare da Gwamnan jihar Taraba Darius Ishaku

Isarsa jihar Taraba ke da wuya akan hanyarsa ta zuwa kasar Ghana, Shugaba Muhammadu Buhari ya zauna da masu ruwa da tsaki a jihar Taraba domin tattaunawa kan yadda za’a shawo kan matsalolin rikice rikicen da suke janyo hasararrayuka da dama a jihar.

Shugaba Buhari ya isa birnin Jalingo na jihar Taraba tare da rakiyar Ministan tsaro Mansur Dan Ali da mataimakin Gwamnan jihar Taraba Haruna Manu, ya samu tarba ta musamman daga Gwamnan jihar Mazayyani Darius Dickson Ishaku.

 

LEAVE A REPLY