A sakamakon rikita rikitar da ta biyo bayan zabubbukan Shugabannin mazabu na jam’iyyar APC mai mulki, da kuma batun jinkirin zartar da kasafin kudin wannan shekarar da majalisun tarayya suka gaza yi, Shugaba Buhari ya yi wani kiran taron gaggawa da Shugabannin Majalisa da suka hada da Saraki da kuma Dogara yau a fadar Gwamnati.

Wani dake bamu labari daga fadar Shugaban kasa ya shai da mana cewar Shugaba Buhari na ganawa da Shugabannin majalisar ne a cikin sirri su uku ba tare da barin ‘yan jaridu su shiga wajen tattaunawar tasu ba.

Har ya zuwa yanzu dai ba’a samu tabbacin abinda suke tattaunawa akai ba. Zamu kawo muku karin bayani an jima.

LEAVE A REPLY